11 Faburairu 2022 - 13:10
‘Yan Adawan Mali Zasu Yanke Kauna Ga Hukumomin Rikon Kwarya

‘Yan adawa a kasar Mali, sun sanar da cewa zasu yanke kauna ga hukumomin rikon kwarya na kasar daga ranar 25 ga watan Maris mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -kawancen jam’iyyun da ya hada da jiga-jigan jam’iyyu na kasar sun kuma bada wasu shawarwari na fitar da kasar daga cikin halin da take ciki.

Bangarorin sun kuma bukaci a kafa wata sabuwar gwamnatin wucin gadi wacce wani firaminista marar bangaranci zai jagoranta.

342/